Kada ku zabi wadanda zasu mayar da ofishin gwamna wajen rawar nanaye – Oshiomhole ya gargadi mutanen Osun

Kada ku zabi wadanda zasu mayar da ofishin gwamna wajen rawar nanaye – Oshiomhole ya gargadi mutanen Osun

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, a ranar Talata, 18 ga watan Satumba, ya kaddamar da cewa Jihar Osun bata cancanci dan koyo a matsayin gwamna ba zai wanda zai iya gudu a tseren.

Oshiomhole ya fadi hakan lokacin da jiga-jigan jam’iyyar karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari suka isa jihar Osun domin yin gangamin karshe don tabbatar da nasarar dan takaransu, Isiaka Oyetola a zaben gwamna da za’a gudanar a jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Oshiomhole yace gwamnati ba wajen da mutun zai koyi aiki bane.

Kada ku zabi wadanda zasu mayar da ofishin gwamna wajen rawar nanaye – Oshiomhole ya gargadi mutanen Osun

Kada ku zabi wadanda zasu mayar da ofishin gwamna wajen rawar nanaye – Oshiomhole ya gargadi mutanen Osun
Source: Depositphotos

Ya gargadi mutanen Osun kan cewa kada su zabi gwamnan da zai mayar da ofishin gwamna wajen rawar ýan nanaye.

Da farko dai munji cewa a ranar Talata, 18 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin jahar Osun, Osogbo don halartar babban gangamin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar na jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Jirgin bincike na dakarun Rasha ya bata a teku

Buhari ya halarci wannan gangami ne don mara ma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar dake karatowa, Isiaka Oyetola, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Osun.

Legit.ng ta ruwaito sai da Buhari ya fara sauka a filin sauka da tashin jirage dake garin Ibadan na jahar Oyo inda gwamnan jahar, Isiaka Abiola Ajimobi ya tarbe shi, kafin daga nan ya wuce garin Osogbon jahar Osun inda gwamnan jahar Rauf Aregbesola ya tarbe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel