Aukuwar wani hari ta salwantar da rayukan Mutane 4 a jihar Filato

Aukuwar wani hari ta salwantar da rayukan Mutane 4 a jihar Filato

Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda reshen jihar Filato, ta bayar da tabbacin salwantar rayukan wasu mutane uku da tuni aka yi jana'izarsu a garin Gyel dake karamar hukumar Jos ta Kudu a ranar Lahadin da ta gabata.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Tyopev Terna, shine ya bayar da tabbacin wannan rahoto cikin wata sanarwa da ya bayyana yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Talata.

Rahotanni kwanaki kadan da suka gabata sun bayyana cewa, harin da wasu 'yan bindiga suka zartar a karamar hukumar Bassa ta jihar, ya salwantar da rayuwar wata mata da kuma Maza biyu, sai dai hukumar 'yan sanda ba ta bayar da tabbacin ta akan lamarin ba.

Aukuwar wani hari ta salwantar da rayukan Mutane 4 a jihar Filato

Aukuwar wani hari ta salwantar da rayukan Mutane 4 a jihar Filato
Source: Facebook

Kazalika rahoton ya bayyana cewa, kimanin mutane uku sun jikkata yayin aukuwar wannan hari da wasu 'yan bindiga suka zartar.

KARANTA KUMA: Amfani 6 na Man Lemun tsami ga Lafiyar 'dan Adam

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar 17 ga watan Agustan da ta gabata ne wasu matasa suka kai munanan hari na ta'addanci kololuwa kan wasu yankuna a jihar ta Filato da suka salwantar da rayukan mutane da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar 'yan sandan jihar ta baza jami'anta tare da umartarsu da tsayuwar daka wajen bankado wannan miyagu dake kawo zagon kasa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel