Hanyar lafiya: Bukar ya bi sahun abokinsa Yarima, ya janye takararsa ta kujerar sanata

Hanyar lafiya: Bukar ya bi sahun abokinsa Yarima, ya janye takararsa ta kujerar sanata

Sanata mai wakiltar jihar Yobe ta gabas a majalisar dattijai, Bukar Abba, ya bayyana cewar ya janye takararsa a zaben 2019 domin bawa gwamnan jihar, Ibrahim Geidam, dama.

Bukar, tsohon gwamnan jihar Yobe, ya bayyana hakan ne yau, Talata, yayin wata ziyara da ya kaiwa gwamna Geidam a gidan gwamnatin Yobe dake unguwar Asokoro a Abuja.

Sanatan ya bayyana cewar ya yanke shawarar janye takararsa ne domin cika alkawarin da ya dauka na cewar ba zai yi takara ba matukar gwamna Geidam na sha’awar yin takarar kujerar sanatan gabashin Yobe.

Kazalika ya bayyana cewar zai goyi bayan dan takarar gwamnan APC a jihar Yobe, Mai Mala Buni, dan takarar da Geidam ya zaba domin ya maye gurbinsa.

Hanyar lafiya: Bukar ya bi sahun abokinsa Yarima, ya janye takararsa ta kujerar sanata

Bukar da Gaidam
Source: Twitter

Ita siyasa dama ta gaji samun sabani tsakanin mutum da abokansa da kuma wadanda tafiyar siyasa ta hada su tare. Ba zai yiwu mutum ya samu duk yadda yake so ba. Na dade tare dad an uwana, gwamna Geidam, kuma duk dam un sha samun sabani, hakan ba zai raba mu ba,” a kalaman Bukar.

DUBA WANNAN: Al'ajabi: Wata mata ta haifi jariri mai ido daya tal a tsakiyar goshi, hotuna

Tsohon gwamnan ya kara da cewa shi yanzu burinsa ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a kowanne mataki a zaben shekarar 2019.

Bukar ya zama tsohon gwamna na biyu day a zuwa yanzu suka bayyana janye takararsu ta kujerar sanata domin bawa gwamnonin jihohinsu dama.

A kwanakin baya-bayan nan ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Sani Yarima, ya bayyana janyewa gwamna Abdulaziz Yari takarar kujerarsa ta sanata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel