An nemi Okoi Obla yayi koyi da Ministar kudi Kemi Adoesun ya bar mukamin sa

An nemi Okoi Obla yayi koyi da Ministar kudi Kemi Adoesun ya bar mukamin sa

Mun fara samun labari cewa mutane sun hurowa mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin bincike watau Obono-Obla Okoi yayi murabus daga matsayin da yake kai.

An nemi Okoi Obla yayi koyi da Ministar kudi Kemi Adoesun ya bar mukamin sa

Mutane na neman mai ba Shugaban kasa shawara ya ajiye aikin sa
Source: Depositphotos

An fara taso Okoi Obono-Obla a gaba ne bayan Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ta ajiye mukamin ta bayan ta tabbata cewa ba ta da gaskiya a zargin da ake yi mata na amfani da shaidar takardun bautar kasa na bogi.

Haka dai shi ma Obono-Obla yana amfani ne da shaidar jarrabawar WAEC ta kamalla Sakandare na bogi. Da wannan shaidan karyar ne dai Obono-Obla ya samu shiga Jami’ar Jos har ya karanta ilmin harkar shari’a a Najeriya.

KU KARANTA: Guguwar sauya sheka ta yada zango a majalisar dokokin wata jihar APC

Hukumar ICIR da ke binciken kwa-kwaf a Duniya ta rahoto cewa ana neman Hadimin Shugaban kasar na Najeriya ya bi Ministar kudi Adeosun. Yanzu dai duk da irin gyare-gyaren da Adoesun ta kawowa Kasar ta bar matsayin ta.

Kwanaki wani babban Jami’in WAEC Femi Ola ya tabbatarwa Majalisar Tarayyar kasar cewa satifiket din Obono Obla na jabu ne. Shugaban makarantar kwarewa a harkar shari’a Isa-Hayatu Chiroma ya tabbatar da wannan kwanaki.

A shekarar 1982 ne Obono-Obla ya rubuta jarrabawar WAEC inda aka ce bai rubuta takardar Ingilishi. Amma a sakamakon sai ga shi ya samu lashe jarrabawar Ingilishi.Hakan ta sa aka fara kira Hadimin na Buhari yayi murabus.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel