Guguwar sauya sheka ta yada zango a majalisar dokokin wata jihar APC

Guguwar sauya sheka ta yada zango a majalisar dokokin wata jihar APC

- 'Yan majalisar dokoki na jiha Osun guda biyar sun fice daga jam'iyyunsu sun sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun

- Cikin wadanda suka sauya shekar har da Kakakin majalisar da shugaban marasa rinjaye na majalisar

- Wannan sauyin sheka na zuwa ne kwanaki kadan kafin gudanar da zaben gwamna a jihar ta Osun

Wasu 'yan majalisar dokoki na jihar Osun sun sauya sheka zuwa wasu jam'iyoyi ciki har da Kakakin majalisar jihar, Mr Olagunji Ojo, Shugaban marasa rinjaye, Mr Ademola Ige, da wasu 'yan majalisar guda uku duk a yau Talata.

Magatakardan Majalisar, Mr Paul Bankole ne ya karanto wasikun sauya shekan daya bayan daya a zaman majalisar da akayi a Ibadan.

APC da ADC sun samu karuwa a jihohin yammacin Najeriya

APC da ADC sun samu karuwa a jihohin yammacin Najeriya
Source: Twitter

Wandanda suka sauya sheka daga Labour Party zuwa APC sun hada da Kakakin majalisa Mr Olagunji Ojo (Orire), Mrs Wunmi Oladeji (Ogbomoso ta Arewa) da Solomon Olukoya (Ogbomoso South).

DUBA WANNAN: Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Gbenga Oyekola mai wakiltan Atiba ya sauye sheka daga Labour Party zuwa African Democratic Congress (ADC) shi kuma Peter Oyetunji mai wakiltan Adiba yakuma ya fice daga Labour Party ya koma PDP.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Mr Ademola Ige da ke Accord Party da Mr Fatai Adesina na Accord Party duk sun sauya sheka zuwa African Democratic Congress (ADC)

Har ila yau, majalisar dakokin jihar tayi kira ga Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Abiodun Odude ta dauki matakin kawo karshen tashe-tashen hankula da ke afkuwa a birnin Oyo ta hanyar aikewa da 'yan sandan da za su iya magance matsalar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel