Hukumar INEC ta haramta zuwa wurin zabe da wayar salula

Hukumar INEC ta haramta zuwa wurin zabe da wayar salula

Hukumar zabe mai zaman kanta ta haramta zuwa wurin kada kuri'a da wayar salula.

Kakakin hukumar zaben, Malam Aliyu Bello ne ya ntabbatar da hakan sannan kuma ya kara da cewa hukumar ta yanke wannan hukunci ne saboda yin maganin matsalar magudin zabe.

A cewar Bello, wannan mataki zai fara aiki ne a zaben jihar Osun da za’a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

"Yin haka na daga cikin matakai da hukumar zabe ta dauka domin ta rage barna da ake tafkawa a daidai lokacin da ake kada kuri'a... hukumar na kokarin gano dabaru da salon yadda za a gudanar da zabe nagartacce ne," cewar shi.

Hukumar INEC ta haramta zuwa wurin zabe da wayar salula

Hukumar INEC ta haramta zuwa wurin zabe da wayar salula
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa a nasu fahimtar, masu sayar da kuri'unsu suna kulla yarjejeniya ta yadda masu sayar da kuri'a za su nuna wa masu sayen wata shaida da za ta gamsar da su cewa jam'iyyarsu mutum ya jefawa kuri’’a kafin su biya shi saboda haka, wannan mataki zai kawo karshen lamarin.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP

Ya kuma yi kira ga al’umman kasar su ba su hadin kai wajen ganin sun gabatar da dokar ba tare da fuskantar matsaloli ba.

A halin da ake ciki, mun ji cewa a ranar Talata, 18 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin jahar Osun, Osogbo don halartar babban gangamin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar na jam’iyyar APC.

Buhari ya halarci wannan gangami ne don mara ma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar dake karatowa, Isiaka Oyetola, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Osun.

Legit.ng ta ruwaito sai da Buhari ya fara sauka a filin sauka da tashin jirage dake garin Ibadan na jahar Oyo inda gwamnan jahar, Isiaka Abiola Ajimobi ya tarbe shi, kafin daga nan ya wuce garin Osogbon jahar Osun inda gwamnan jahar Rauf Aregbesola ya tarbe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel