Dalilin da ya sa na marawa Jonathan baya a zaben 2015 – Tanko Yakassai

Dalilin da ya sa na marawa Jonathan baya a zaben 2015 – Tanko Yakassai

Labari ya zo mana cewa Dattijon nan na Yankin Arewa watau Dr. Tanko Yakassai ya fito ya bayyana dalilin da ya sa ya marawa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan baya a zaben 2015.

Dalilin da ya sa na marawa Jonathan baya a zaben 2015 – Tanko Yakassai

Tanko Yakassai yace akwai hikimar da ta sa ya bi Jonathan
Source: Depositphotos

Kwanan nan ne Dattijon na Arewa yayi wani dogon jawabi kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard inda yace babban taron nan na CONFAB ta Jonathan ya shirya ne ya sa ya goyi bayan sa a zaben da ya wuce.

Tanko Yakassai yace ya marawa Jonathan baya duk da bai taba yin ido-hudu da Shugaban kasar ba. A jawabin da Yakassai yayi, ya bayyana cewa ya ga akwai bukatar mutanen Arewa su kulla alaka mai kyau da ‘Yan Neja-Delta.

Fitaccen Dattijon da ya dade a harkar siyasa yace akwai kwantacciyar gaba tsakanin Yarbawa har ma da Inyamurai da Hausawa don haka ya nemi a samu dangantaka mai kyau tsakanin Mutanen Arewa da Kabilun Neja-Delta.

KU KARANTA: Zan cigaba da yin adalci a kan karagar mulki - Buhari

Kabilun na Neja-Delta dai su na cikin wadanda ake nunawa karfi duk da arzikin fetur da su ka mallaka don haka ne Yakassai yace ya ga hikimar bin su Jonathan a baya domin duk an yi wa Yankunan nisa a Najeriya.

A wajen taron da aka shirya, Yakassai wanda ya taba zama mai ba tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari shawara yace an yi wa Hausawa da Mutanen Yankin Neja-Delta na su Jonathan fin-tin-kau tun bayan Yakin basasa.

A baya jun ji cewa Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal wanda yana cikin ‘Yan takaran PDP ya a zabe sa domin ya kawo karshen rabuwar kai a Najeriya. A baya Tambuwal din yace su su ka daura Jonathan kan mulki a 2010.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel