Takara daga gidan yari: Fursuna kuma tsohon gwamna, Dariye, ya mayar da fam dinsa na takarar Sanata

Takara daga gidan yari: Fursuna kuma tsohon gwamna, Dariye, ya mayar da fam dinsa na takarar Sanata

Sanata mai wakiltar jihar Filato ta tsakiya, Joshua Dariye, ya mayar wa da jam’iyyar APC fam dinsa na takarar kujerar sanata a zaben shekarar 2019.

Yanzu haka Mista Dariye na gidan bayan wata kotun Najeriya ta yanke masa daurin shekaru 14 saboda samun sa da laifin almundahanar kudi lokacin da yake gwamna a jihar Filato.

A yau, Talata, ne Chindo Dafat, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Filato, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a garin Jos cewar Dariye ya kamala cike fam dinsa na takarar sanata kuma ya mayarwa da jam’iyyar ta APC.

Takara daga gidan yari: Fursuna kuma tsohon gwamna, Dariye, ya mayar da fam dinsa na takarar Sanata

Joshua Dariye
Source: Depositphotos

Sakataren APC na mazabar Dariye ne ya saka hannu kan fam din takarar a madadin tsohon gwamnan. Ya cike fam din, an dawo da shi kuma tuni magoya bayansa suka fara yi masa yakin zabe,” a cewar Dafat.

A cewar Dafat, tsohon gwamna Dariye zai fafata da ragowar ‘yan takarar kujerar a karkashin jam’iyyar APC su uku; Zakari Dimka, Sam Piwuna da Manji Pompori.

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya lisafa 'yan Najeriya 4 da suka fi Buhari gaskiya da rikon amana

A kan halaccin takarar ta Dariye, Dafat y ace “babu wata doka da ta hana shi sayen fam. Har yanzu Dariye na da magoya baya masu dumbin yawa duk da halin da yake ciki kuma muna fatan kotun gaba zata wanke shi tunda ya daga kara. Muna yi masa addu’a.”

Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana wannan lamari a matsayin babban abun mamaki day a girgiza ta, kamar yadda Ben Shignugul, mataimakin shugaban PDP a Filato ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel