'Yan bindiga sun budewa motar yan sanda wuta, sun kwasa bindigu

'Yan bindiga sun budewa motar yan sanda wuta, sun kwasa bindigu

- Wasu 'yan bindiga sun budewa motar 'yan sanda wuta a Asaba

- Sun kashe dan sanda guda tare da raunata sauran 'yan sandan

- Sun kuma kwashe bindigogi biyu kirar AK 47

Hankula sun tashi a Asaba, babban birnin Jihar Delta bayan wasu gungun 'yan bindiga sun kaiwa wasu 'yan sanda da ke sintiri a motarsu farkmaki har suka kashe guda cikin 'yan sandan a safiyar yau Litinin.

'Yan bindiga sun far wa motar 'yan sanda, sun kashe guda

'Yan bindiga sun far wa motar 'yan sanda, sun kashe guda
Source: Depositphotos

Punch ta ruwaito cewa 'yan bindigan sunyi musayar wuta da jami'an 'yan sandan misalin karfe 8.26 a unguwar Cable Point, hakan yasa Bankuna da sauran masu gudanar da kasuwanci suka rufe wuraren sana'o'insu.

DUBA WANNAN: Tawagar gwamnan APC tayi hatsari a hanyar zuwa Abuja

Majiyar Legit.ng ta gano cewa 'yan sanda biyar ne ke cikin motar lokacin da 'yan bindigan suka budewa motar wuta.

Har ila yau, majiyar ta ce daya daga cikin 'yan sandan da ya sha da kyar yana nan rai hannun Allah a wata asibiti da ba'a ambaci sunansa ba, an kuma ce 'yan bindigan sun dauke AK 47 guda biyu na 'yan sandan.

Kwamishinan 'yan sandan jihar. Mr Muhammad Mustapha ya tabbar da afkuwar lamarin a lokacin da aka tuntube shi ta wayar tarho.

Ya e jami'an hukumar sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu cikin harin, kuma hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin kai harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel