Buhari ya bayar da umurnin fara wani muhimmin aiki a bangaren sufuri

Buhari ya bayar da umurnin fara wani muhimmin aiki a bangaren sufuri

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin aikin sada dukkan tashoshin ruwan Najeriya da layyukan dogo ta yadda za'a rika jigilar kayayakin da aka sauke a cikin jiragen kasa zuwa sasan kasar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi wajen taron Kungiyar ma'aikatan tashohin jiragen ruwa da akayi a ranar Litinin a Abuja.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen gine-ginen da za su taimaka wajen sufuri daga tashohin ruwa zuwa sauran sassan kasa.

Buhari ya bayar da umurnin fara wani muhimmin aiki a bangaren sufuri

Buhari ya bayar da umurnin fara wani muhimmin aiki a bangaren sufuri
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Tawagar gwamnan APC tayi hatsari a hanyar zuwa Abuja

"Da fari, na umurci a gina layin dogo da zai sada dukkan tashohin ruwa da ke Najeriya da sauran sassan kasar. Burinmu shine daga shekarar 2021, za mu samar da layyukan dogo daga Kudu zuwa Arewa saboda bunkasa kasuwanci." inji Buhari.

Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa tana gudanar da ayyukan tituna a dukkan yankunan Najeriya, "A halin yanzu, muna gyarar manyan tituna 25 da kuma wasu tagwayen hanyoyi 44 a shiyoyin siyasa shida na kasar kamar yadda muke aikin farfado da hanyoyin ruwa."

A wata, rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa majalisar dokokin jihar Kano da tabbatar da nadin Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Kafin nadinsa, Gawuna shine kwamishinan ayyukan Noma da raya karkara a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel