2019: PDP a jihar Legas ta tsaida Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa

2019: PDP a jihar Legas ta tsaida Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa

- Magoya bayan PDP a jihar Legas, sun tsayar da Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar zaben 2019 da ke gabatowa

- Saraki ya yi masu alkawarin cewa idan har zaben 2019 ya zo, PDP za ta kwace gidan gwamnati na Alausa

- Sakataren jam'iyyar PDP na jihar, Mr. Muiz Dosunmu, ya baiwa Saraki tabbacin goyon bayansu dari bisa dari

A yayin da tseren samun tikitin takarar shugaban kasa ya yi kamari a jam'iyyar PDP, magoya bayan jam'iyyar a jihar Legas, sun tsayar da shugaban majalisar dattijai, Dr. Bukola Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar.

Mambobin jam'iyyar sun yanke wannan hukunci ne bayan da aka bukace su da su zabi Saraki a matsayin dan takararsu, kasancewar shi cikakken dan asalin jihar Legas ne, duba da cewa a nan ne aka haife shi har ya yi karatunsa a jihar, ya cancanci goyon bayan su, ga shi kuma ya shaida masu cewa a yanzu kasar na bukatar shugaban da zai jagoranci jama'a cikin kwarewa.

Saraki wanda ya je sakatariyar jam'iyyar PDP ta jihar Legas a ci gaba da ran gadin tuntuba da ya ke yi na samun tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, ya ce la'akari da nagartattun mutanen da ke a jam'iyyar ta jihar, ba shi da haufi kan nasarar PDP a zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Yanzu Yanzu: IBB da Orji Kalu sun shiga ganawar sirri a Minna

2019: PDP a jihar Legas ta tsaida Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa

2019: PDP a jihar Legas ta tsaida Saraki a matsayin dan takarar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Ya sha alwashin cewa idan har zaben 2019 ya zo, PDP za ta kwace gidan gwamnati na Alausa; ya yin da ya ke kara yi masu alkawarin cewa "abubuwan da kuke yaki akan ganin sun tabbata, za su tabbata a 2019."

Daga cikin shuwagabannin jam'iyyar da suka raka Saraki zuwa sakatariyar akwai Sanata Dino Melaye, Dr. Ade Dosunmu; tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Sanata Kofo Akerele-Bucknor, Mr. Deji Doherty, tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, Dr. Doyin Okupe da kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Kawu Baraje, da dai sauransu.

Saraki ya ce lokaci ya yi da za'a canja wasu abubuwan na kasar, yana mai cewa an kawo bukatar sake fasalin kasar ne ga shugaban da ya gaza gane manufar sake fasali da bun kasa kasar.

Ya bata tabbacin cewa akwai wasu bangarori na kasar, da mazauna garuruwan ba su ma san suna rayuwa a cikin kasar ba, saboda rashin samun adalin shugaba da gwamnati mai nuna halin ko in kula da rayuwar jama'ar kasar.

Da ya ke maida jawabi, sakataren jam'iyyar PDP na jihar, Mr. Muiz Dosunmu, ya baiwa Saraki tabbacin goyon bayansu dari bisa dari, tare da yi masa fatan alkairi a kudurin da ya sanya a gaban sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Zaben 2019: Shin Saraki zai iya zama shugaban kasar Nigeria na gaba? | Legit.ng TV

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel