Yan bindiga sun hallaka wani tsoho dan shekara 62, sun jikkata 3 a Filato

Yan bindiga sun hallaka wani tsoho dan shekara 62, sun jikkata 3 a Filato

Rundunar Yansandan jahar Filato ta sanar da kisan wani dattijo mai shekaru sittin da biyu a rayuwa mai suna John Atu da wasu gungun yan bindiga suka aikata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kashe wannan tsoho ne a yayin da suka kai farmaki a kauyen kwall dake yankin Miango cikin karamar hukumar Bassa na jahar Filato, haka zalika sun raunata mutane uku.

KU KARANTA: Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa

Kaakakin Yansandan jahar, Terna Tyopev ne ya tabbatar da haka a ranar Talata 18 watan Satumba garin Jos, inda yace yan bindigan sun kai harin ne a daren Litinin:

Yan bindiga sun hallaka wani tsoho dan shekara 62, sun jikkata 3 a Filato

Kisa a Filato
Source: Depositphotos

“Da misalin karfe 8 na safiyar Litinin ne wnai shugaban matasan Kwall, Robert Zarachi ya bamu rahoton hari da yan bindiga suka kai da misalin karfe 10:45 na daren Litinin zuwa gidan John Atu mai shekaru 62. A sakamakon wannan hari ne Atu ya gamu da ajalinsa, sa’annan wasu yayansa gud uku suka samu munana rauni a sanadiyyar harbe harben bindiga.” Inji shi.

Sai dai Kaakakin Yansandan yace tuni aka yi jana’izar John kamar yadda al’adun kabilar Irigwe ta tanadar, yayin da sauran yan uwannasa ke samun kulawa a Asibitin Enos dake garin Miango, daga karshe yace tun suka fara gudanar da bincike don kama maharan.

A wani labarin kuma, DSP Terna yace jami’an rundunar Yansandan jahar Filato sun samu nasarar kama mutane da suka kashe mutane uku a garin Gura Riyom dake karamar hukumar Jos ta kudu, inda ya bayyan sunayen wadanda aka kashe kamar haka; Aminu Angara, Aisha Musa da Daniel

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel