Yanzu Yanzu: IBB da Orji Kalu sun shiga ganawar sirri a Minna

Yanzu Yanzu: IBB da Orji Kalu sun shiga ganawar sirri a Minna

- An saka labule tsakanin IBB da DR. Orji Uzor Kalu

- Wannan ganawar sirrin na faruwa ne a gidan alfarma na IBB da ke Minna, babban birnin jihar Niger

- Har zuwa yanzu ba'a san dalilin wannan ganawar ta su ba

Rahotannin da Legit.ng ta ke samu yanzu na nuni da cewa an saka labule tsakanin tsohon shugaban Nigeria a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma tsohon gwamnan jihar Abia, wanda kuma jigo ne a jam'iyyar APC, DR. Orji Uzor Kalu.

Wannan ganawar sirrin na faruwa ne a gidan alfarma na IBB da ke Minna, babban birnin jihar Niger.

JIgo a jam'iyyar ta APC, Sanata Orji Kalu ya isa gidan IBB da misalin karfe 12:08 na rana, tare da bakaken motoci 3 kirar Lexus SUVs da kuma kirar Hillux guda 2, dauke da jami'an tsaro da jama'arsa da suka mara masa baya.

KARANTA WANNAN: Mu muka yaudari Jonathan a 2015: Akpabio ya shaidawa Buhari

Yanzu Yanzu: IBB da Orji Kalu sun shiga kanawar sirri a Minna

Yanzu Yanzu: IBB da Orji Kalu sun shiga kanawar sirri a Minna
Source: Twitter

Dr. Kalu da tawagarsa sun samu marafta, idan aka kaisu dakin tarbar baki da ke cikin gidan tsohon shugaban kasar.

Kafin tsohon gwamnan da tsohon shugaban kasar su saka labule, an bukaci 'yan rakiyar Dr. Kalu da su baiwa shuwagabannin biyu wuri don samun sararin ganawa.

Har zuwa yanzu ba'a san dalilin wannan ganawar ta su ba.

Cikakken rahoton na zuwa maku anjima...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Shin Ambode zai iya samun tazarce ba tare da amincewar Tinubu ba? | NAIJ TV

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel