Da duminsa: Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano

Da duminsa: Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano.

Yan majalisan sun tabbatar da shi ne bayan tattaunawa da shi da yau Talata, 18 ga watan Satumba, 2018.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, bisa ga murabus din tsohon gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar. Za’a rantsar da Nasiru Gawuna a yau.

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi kwamishanan aikin noma, Nasiru Gawuna, a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Da duminsa: Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano

Da duminsa: Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da Gawuna a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano
Source: Twitter

Kimanin wata daya kenan da Ganduje ke shugabancin jihar ba tare da mataimaki ba tun lokacin da tsohon mataimakin farfesa Hafiz Abubakar yayi murabus ranan 5 ga watan Agusta.

An zabi Malam Nasiru Gawuna wanda tsohon shugaban karamar hukuma ne kuma shugaban kungiyar wasannin matasan Najeriya cikin mutani hudu da gwamnan ke kokarin zaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel