Mu muka yaudari Jonathan a 2015: Akpabio ya shaidawa Buhari

Mu muka yaudari Jonathan a 2015: Akpabio ya shaidawa Buhari

- Sanata Godwill Akpabio, ya tona asirin yadda suka yaudari tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babban zaben 2015

- Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wa su da ga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC zuwa ziyara ga shugaban kasa Buhari

- Ya yi ikirarin cewa tsawon shrkaru 16 da jam'iyyar PDP ta kwashe a saman mulki, ba a aiwatar da wani aikin gwamnatin tarayya a jihar Akwa Ibom ba

Sanata Godwill Akpabio, tsohon gwmanan jihar Akwa Ibom, ya tona asirin yadda shi da wasu mambobin jam'iyyar adawa ta PDP suka yaudari tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a babban zaben 2015.

Da ya ke jawabi a kashin kansa, ya ce ko a zaben 2015, zuciyarsa na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma gudun zargin jama'a da kuma tsoron kada a zarge shi da juyawa jam'iyya baya, ya sa shi dole boye soyayarshi ga Buhari.

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wa su da ga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC a Akwa Ibom zuwa ziyara ga shugaban kasa Buhari a fadar sa da ke Abuja, a ranar litinin.

KARANTA WANNAN: Wani dan kasar Morocco ya zo Nigeria a kan Keke don yawon bude ido

Sanata Godswill Akpabio

Sanata Godswill Akpabio
Source: Depositphotos

Akpabio, wanda ya baya baya nan ya sauya sheka zuwa APC, ya yi ikirarin cewa tsawon shrkaru 16 da jam'iyyar PDP ta kwashe a saman mulki, ba a aiwatar da wani aikin gwamnatin tarayya a jihar Akwa Ibom ba.

Ya kuma bugi kirji da cewar jihar Akwa Ibom ce za ta zamo ta farko a jihohi Kudu-maso-Kudu da jam'iyyar APC zata samu nasara a babban zaben 2019.

Ya shaidawa shugaban kasa Buhari cewa akalla mutane 260,000 ne suka yi rejista a matsayin sabbin shiga jam'iyyar APC a jihar, biyo bayan sauya shekarsa, tare da cewa adadin mutanen na iya karuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel