Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

- Shugaba Buhari yayi alkawarin cewa zai cigaba da yin adalci da daidaito wajen nade-naden mukamai

- Ya kuma sha alwashin yin ayyukan ci gaba a jihar Akwa Ibom dama yankin kudancin kasar baki daya

- Buhari yayi wannan alkawari ne yayinda ya karbi bakuncin dattawan jihar Akwa Ibom

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba yayi alkawarin cewa zai cigaba da yin adalci da daidaito wajen nade-naden mukamai daban-daban a gwamnatinsa.

Gidan talbijin din Channels ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wannan alkawarin ne a yayin wani tattaunawa da tawagar shugabanni da dattawan Akwa Ibom da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari
Source: UGC

“Na lura da godiyarku akan nade-naden mutanen jiharku da aka yi a gwamnatin tarayya.

“Na baku tabbacin cewa zan cigaba da yin adalci da daidaito a wajen nade-naden mukaman tarayya a dukkanin jihohin dake fadin kasar.”

KU KARANTA KUMA: Maye gurbin Adeosun da Zainab Ahmad: Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta caccaki Buhari

Shugaban kasar ya kuma sha alwashin yin Karin ayyukan ci gaba a jihar na Akwa Ibom da kudacin kasar baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel