Maye gurbin Adeosun da Zainab Ahmad: Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta caccaki Buhari

Maye gurbin Adeosun da Zainab Ahmad: Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta caccaki Buhari

Kungiyar mabiya addinin Kirista a Najeriya wato CAN ta sake caccakan shugaba Muhammadu Buhari da fifita Musulmai daga Arewacin Najeriya wajen manyan nade-naden mukaman gwamnati.

Kungiyar CAN ta yi wannan suka ne musamman ka wasu nade-nade da Buhari yayi a kwanakin bayan nan.

A wata jawabi da kungiyar ta saki jiya Litinin, shugaba kungiyar CAN, Samson Ayokunle, ya jaddada zargin da yakewa shugaba Buhari cewa bangaracin da yake nunawa wajen nade-nade ya sabawa ka’idojin hadin kan Najeriya.

KU KARANTA: Zan koya muku yadda zaku kada Tinubu a jihar Legas – Bukola Saraki

Jawabin yace:“Buhari a ranan 1 ga watan Satumbaya nada Abbas Umar a matsayin shugaban kamfanin biga kudaden Najeriya, kana a ranan 13 ga watan Satumba ya sake nada Yusuf Magaji Bichi daga jihar Kano domin maye Matthew Sayeifa daga jihar Bayelsa wanda yake rikon kwarya tun lokacin da aka salami Lawal Daura.”

“A ranan 14 ga watan Satumba kuma, ya sake nada Zainab Ahmad matsayin mukkadashiyar ministan kudi domin maye gurbin Kemi Adeosun wacce tayi murabus.”

Gwamnatin tarayya ta cigaba da karyata zarge-zargen da ake cewa shugaba Buhari na nuna bangaranci wajen nade-nade. An bukaci masu wannan suka su dubi dukkan nadin da yayi daga hawa mulkinsa.

Amma duk da wannan bayani da fadar shugaban kasa keyi, kungiyar Kiristocin Najeriya basu gamsu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel