Zan koya muku yadda zaku kada Tinubu a jihar Legas – Bukola Saraki

Zan koya muku yadda zaku kada Tinubu a jihar Legas – Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Dr Bukola Saraki, ya kai ziyaran yakin neman zabensa jihar Legas da Ogun da jiya Litinin, 18 ga watan Satumba 2018.

Saraki ya bayyanawa mambobin jam’iyyar PDP a jihar Legas cewa zai yi iyakan kokarinsa wajen tabbatar da cewa PDP ta lashe kujeran gwamnan jihar a zaben 2019.

Shugaban majalisan dattawan ya yi magana ne sakatariya jam’iyyar PDP na jihar Legas inda suka nuna masa goyon bayansu kuma matsayin wanda zasu zaba musamman lokacin da yake yanada maganin mutumin da ikirarin jihar Legas tasa ne.

Zan koya muku yadda zaku kada Tinubu a jihar Legas – Bukola Saraki

Zan koya muku yadda zaku kada Tinubu a jihar Legas – Bukola Saraki
Source: Depositphotos

Yace: “Abinda kuka dau shekaru kuna nema, za ku same shi a zaben nan mai zuwa saboda a yanzu kunada mutum wanda ke da niyyar yakan wadanda ke takura muku.”

“Inada maganin mutumin nan (Tinubu) wanda yake dauka kansa uban kowa da ke ta’addanci a jihar Legas. Mun san abinda sukeyi, a shekara mai zuwa, jam’iyyar PDP zata kwace Legas,”.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN

Saraki ya gargadi yan Najeriya da suyi hattara da yan takaran shugaban kasa dake musu alkawarin sauya fasalin kasa idan aka zabesu. Ya ce aikin garambawul ba abu bane da shugaban kasa zai iya aiwatarwa bas hi kadai ba tare da sa hannun majalisa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel