Kishin-kishin: DSS sun damke mutumin da ya dare kan karfe saboda wahalar mulkin APC

Kishin-kishin: DSS sun damke mutumin da ya dare kan karfe saboda wahalar mulkin APC

Labari ya zo mana cewa yanzu haka Jami’an tsaro sun yi ram da wanda ya hau saman wani dogon karfe ya daina ci da sha kwanaki domin ya nunawa Duniya rashin jin dadin sa da Gwamntin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kishin-kishin: DSS sun damke mutumin da ya dare kan karfe saboda wahalar mulkin APC

An yi kwana 3 an rasa inda Iliyasu ya shiga tun bayan da aka kama sa
Source: Depositphotos

Mun ji kishin-kishin din cewa Jami’an DSS masu fararen kaya sun daure wani Bawan Allah mai suna Nura Iliyasu da ya hau saman wani karfe domin yi wa Gwamnatin APC bore inda yace ta jefa jama’a cikin wahala a kasar nan.

Yanzu labarin da mu ke samu daga Shugaban kungiyar Convene Nigeria watau Adeyanju Deji shi ne Jami’an DSS su azabtar da wannan Bawan Allah kuma an shirya maida shi zuwa Hedikwatar Hukumar da ke cikin Garin Abuja.

KU KARANTA: Sanatan APC ya ba sabon Shugaban Hukumar DSS wasu manyan sirrin aiki

Jaridar LeadersNG ta rahoto cewa ana muzgunawa wannan Matashi inda ake neman ya fadi sunan wadanda su ka shi yayi wannan danyen aiki na hawa saman wani karfe na tsawon kwanaki. Har yanzu dai DSS tayi tsit game da batun.

Iliyasu mai shekaru 28 ya nuna cewa abubuwa sun cabe a Najeriya don haka akwai bukatar a samu wani ‘Dan siyasa irin su Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Bukola Saraki ko Aminu Tambuwal ya dare kujerar Shugaban kasa a 2019.

Kun ji cewa Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya soma yakin neman zaben shugaban kasa yana mai neman Jama’a su zabe sa domin ya kawo karshen talauci da yunwar da jama’a su ke ciki yanzu a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel