EFCC da Jami’an Kwastam sun yi wa Fayose kofar-raggo

EFCC da Jami’an Kwastam sun yi wa Fayose kofar-raggo

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta aike wa Hukumar Kwastan ta Najeriya da wasika kan cewa su sanya idanu sosai a kan duk wani motsi na Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose domin hana shi ficewa daga kasar jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar ta rubuta wasikar ne a ranar 12 ga watan Agusta, inda ta ja kunnen kwastam kan cewa Fayose barazana ne ga zirga-zirga, kuma zai iya ficewa daga kasar nan, ko ta sama, ko ta ruwa ko ma ta kan iyakoki ta kasa.

Gwamna Fayose dai zai cika wa’adin mulkinsa na shekarun hudu a matsayin gwamna a karo na biyu, a ranar 16 ga watan Oktoba.

EFCC da Jami’an Kwastam sun yi wa Fayose kofar-raggo

EFCC da Jami’an Kwastam sun yi wa Fayose kofar-raggo
Source: Depositphotos

Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya sanar wa hukumar kwastam a Abuja cewa Fayose ya na fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da hadin-baki, makarkashiya, kin bin tsarin aikin ofis, rashawa da cin hanci, sata da kuma karkatar da kudade.

KU KARANTA KUMA: An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna

A nata bangaren, hukumar kwastam ta aike wasika ga jami'anta, inda ta nemi shiyyoyin ta na fadin kasar nan da su tabbatar da cewa sun tare duk wata hanya da Fayose zai iya bi ya gudu daga kasar nan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) na Ekiti a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ta bayyana cewar da gwamna Ayodele Fayose yayi zai mika kansa ga hukumar EFCC a ranar da zai bar kujerar mulki a matsayin wani tuggu.

Jam’iyyar APC tace lallai gwamnan na kulla wani shiri ne ta yadda zai samu damar guduwa daga kasar cikin sauki.

Jam’iyyar ta hannun babban sakatarenlabaranta, Taiwo Olatunbosun ta dasa ayar tambaya kan dallin da yasa Fayose ya amince da Karin kasafin nairan biliyan 10 da majalisar dokoki jihar ta nema kasa da wata daya kafin saukarsa mulki.

Jam’iyyar ta bayyana shirin Fayose na gurfana a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a matsayin ci gaba mai kyau, sai dai tayi gargadin cewa hakan na iya kasancewa makirci, sanin cewa Fayose ya iya dabaru kuma yana iya shirya gadar zare ga huumar EFCC da suran hukumomin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel