2019: David Mark, Saraki sun raba kan Arewa ta Tsakiya da Majalisar Dokoki ta tarayya

2019: David Mark, Saraki sun raba kan Arewa ta Tsakiya da Majalisar Dokoki ta tarayya

Neman takarar kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ta tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark da kuma Magajin kujerarsa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ta janyo rabuwar kai mai tsanani a kasar nan.

A yayin da zaben fidda gwani na jam'iyyar ke ci gaba da karatowa, hankoron kujerar shugaban kasa ta jiga-jigan biyu ta janyo rabuwar kai ta akidar siyasa a majalisar dokoki ta tarayya da kuma yankin Arewa ta Tsakiya a kasar nan.

Sai dai hankoron kujerar ta manemi na uku daga yankin Arewa ta tsakiya kan takarar kujerar shugaban kasar, Sanata Jonah Jang, ba ta da wani tasiri kan rabuwar kai a yankin da kuma majalisar.

Kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito, naman takarar kujerar ta Sanatan jihar Kano ta Tsakiya, Rabi'u Kwankwaso, ta dauki wani salo mai tasirin gaske da ta mamaye kasar nan duk da ya fito daga yankin Arewa ta Yamma.

2019: David Mark, Saraki sun raba kan Arewa ta Tsakiya da Majalisar Dokoki ta tarayya

2019: David Mark, Saraki sun raba kan Arewa ta Tsakiya da Majalisar Dokoki ta tarayya
Source: Depositphotos

Sauran manema takarar karkashin jam'iyyar sun hadar da; tsohon Mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar, gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Tambuwal, tsohon gwamna jihar Jigawa; Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Sanata Ahmed Makarfi da kuma tsohon Ministan ayyuka na musamman; Alhaji Tanimu Turaki.

KARANTA KUMA: Rashin adalci ke ci gaba da haddasa ta'addanci a Najeriya - Lamido

Rahotanni sun bayyana cewa, ko shakka ba bu neman takara tsakanin Saraki da kuma David Mark ta dauki wani salo mai tsananin gaske wajen kawo rabuwar kai a Arewa ta tsakiya da kuma majalisar dokoki ta kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, ire-iren gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya musamman na jihar Filato, Samuel Lalong da kuma takwaransa na jihar Benuwe, Samuel Ortom, za su taka rawar gani wajen wannan rabuwar kai kasancewar kowanensu akwai inda yake hange ta fuskar akidar goyon baya tsakanin Saraki da kuma David Mark.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel