Zan gyara Imo cikin watanni 7 kuma zan daura Suruki na ya gaje ni – Okorocha

Zan gyara Imo cikin watanni 7 kuma zan daura Suruki na ya gaje ni – Okorocha

Gwamnan Jihar Imo da ke shirin barin gado wtaau Rochas Okorocha ya kara tabbatar da cewa Uche Nwosu zai zama Gwamnan gobe a Jihar. Uche Nwosu dai yana auren ‘Diyar Gwamnan ne.

Zan gyara Imo cikin watanni 7 kuma zan daura Suruki na ya gaje ni – Okorocha

Okorocha yace zai gyara hanoyi kafin ya kammala wa'adin sa
Source: Depositphotos

A jiya ne Gwamnan ya nada wasu sababbin mukarrabai a Gwamnatin sa inda ya bayyana cewa Uche Nwosu zai zama Gwamna bayan sa. Rochas Okorocha zai karasa hanyoyi da makarantun da bai gama ba a fadin Jihar ta Imo.

Gwamnan yace yace idan har Uche Nwosu ya samu mulki ba zai tsaya bata lokaci wajen gina tituna a Jihar Imo ba. Okorocha yace a Jihar Imo ba a samu wanda ya mika mulki ga wanda yak e so ba, amma za a fara a kan sa.

KU KARANTA: 2019: Ana rikici a wasu manyan Jihohin Jam’iyyar APC

Gwamnan dai ya nada sababbin mukamai a jiyan wanda su ka hada da Ijeoma Ignoanusi, Victor Onyekwere da kuma sabon Sakataren Gwamnati Mark Uchendu. Gwamna ya tsige Surukin na sa Nwosu daga Gwamnati kwanan nan.

Mataimakin Gwamna Okorocha watau Eze Madumere ya nuna masa cewa ba zai yarda da annan shiri da Gwamnan yake yi na ganin Mijin Diyar sa ya gaje sa. Akwai sauran masu harin kujerar Gwamnan a APC irin su Chima Anozie.

Gwamna mai-shirin barin gado Rochas Okorocha duk ya ce zai kammala ayyukan da su ka rage masa a cikin watanni 7 da su ka rage masa. Gwamnan ya caccaki sauran 'yan siyasar Jihar inda yace ba za su kai labari a 2019 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel