Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja

Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja

- Akalla mutane 2,700 daga APC ne suka sauya sheka zuwa PDP a karamar hukumar Kuje

- Sun sha alwashin baiwa PDP dukkanin goyon bayan da take bukata.

- Shugaban jam'iyyar PDP a Abuja, Alhaji Ibrahim Biko, ya jinjina masu bisa wannan hukunci da suka yanke na shiga lemar PDP

Tsofaffin yayan jam'iyya mai mulki ta APC kuma mabiya tsohon gwaman jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar da ubangidansu ya koma ta PDP a karamar hukumar Kuje.

Da ya ke jawabi a madadin wadanda suka sauya shekar, da adadinsu ya kai 2,700, shugaban kungiyar Kwankwasiyya na yankin, Alhaji Musa Hassan Shama, ya ce sauya shekar ta su ya biyo bayan umurnin ubangidansu Sanata Kwankwaso na cewar duk magoya bayansa su koma PDP tare da shi.

KARANTA WANNAN: Wata babbar kotun Ikeja ta yankewa wasu yan ta'adda 2 hukuncin shekaru 42 a gidan wakafi

Ya ce abun takaici ne ace canjin da suka zaba a 2015 ba shine canjin da suke gani yau ba, illa ma babban kuskure da suka tafka, yana mai cewa da yawan mutane sun tsinci kawunansu a cikin yunwa, talauci da rashin tsaro a karkashin mulkin APC.

Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja

Akalla mutane 2,700 ne suka sauya sheka daga APC zuwa PDP a birnin tarayya Abuja

Sun sha alwashin baiwa PDP dukkanin goyon bayan da take bukata.

Shugaban jam'iyyar PDP a birnin tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Biko, wanda ya karbi wadanda suka sauya shekar, ya jinjina masu bisa wannan hukunci da suka yanke na shiga inuwar lemar PDP.

Ya bukace su, da su saki jikinsu kasancewar yanzu PDP gida ce a gare su, tare da yi masu alkawarin yin adalci ba tare da nuna banbanci tsakaninsu da tsofaffin yayan jam'iyyar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel