Tambuwal ya nemi Jama’a su zabe sa domin ya kawo karshen talauci da yunwa a Najeriya

Tambuwal ya nemi Jama’a su zabe sa domin ya kawo karshen talauci da yunwa a Najeriya

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya soma yakin neman zaben shugaban kasa gadan-gadan inda jirgin sa ya leka Garin Abakalili da ke cikin Jihar Ebonyi domin samun goyon bayan manyan Jam’iyyar PDP.

Tambuwal ya nemi Jama’a su zabe sa domin ya kawo karshen talauci da yunwa a Najeriya

Tambuwal na neman a zabe sa Shugaban kasa a Najeriya domin ya fitar da jama'a daga kangi
Source: Twitter

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai na kasan ya bayyana cewa Gwamnonin PDP akalla 8 da kuma masu zaben ‘Dan takara da-dama su na tare da shi. Bayan Gwamnan ya leka Kudancin Najeriya ya kuma shiga cikin Jihar Kebbi.

Wani na-kusa da Tambuwal ya fadawa Jaridar This Day cewa tsohon Shugaban Majalisar Matashi ne mai jini a jika kuma wanda ya san darajar manya sannan bai da nuna banbanci don haka su ke ganin zai yi mulkin kasar nan a 2019.

KU KARANTA: Rikici ya soma barkewa a APC bayan Tambuwal ya koma PDP

Gwamnan na Sokoto Aminu Tambuwal dai yayi alkawarin gyara kasar nan idan ya karbi mulki inda yake cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya raba kan kasar nan kuma yana nuna karfa-karfa kamar ana mulkin Soja a Gwamnatin sa.

A Jihar Kebbi da ‘Dan takarar ya leka ya nemi manyan PDP su mara masa baya ya tika Buhari da kasa a 2019. Tambuwal yace Buhari ya jefa Jama’a cikin matsanancin yunwa da mugun talauci don haka yake neman ceto al’umma.

Jiya kun ji tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Tarayya Aminu Tambuwal ya bada labarin yadda Goodluck Jonathan ya dare kan mulkin Kasar nan bayan rasuwar Ummaru 'Yaradua.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel