Wani maciji ya cafke kasurgumin barawo jim kadan bayan ya tafka sata

Wani maciji ya cafke kasurgumin barawo jim kadan bayan ya tafka sata

- Wani maciji ya cafke kasurgumin barawo jim kadan bayan ya tafka sata

- Macijin dai ya dauki hankalin mutane

- Lamarin ya auku ne a kasar Uganda

Duniyar nan dai ta mu tabbas tana cike da abubuwan mamaki kamar dai yadda muka samu cewa hausawa na cewa, idan har akwai rai, to kam abubuwan ban mamaki basu gama faruwa ba akan idon mu.

Wani maciji ya cafke kasurgumin barawo jim kadan bayan ya tafka sata

Wani maciji ya cafke kasurgumin barawo jim kadan bayan ya tafka sata
Source: UGC

KU KARANTA: Wani dan luwadi ya zayyana wasu kwanciya da shi a Najeriya

Mun samu dai cewa a 'yan kwanakin nan ne dai wani lamarin da ya dauki hankulan al'umma da dama ya faru a kasar Uganda dake a nahiyar Afrika inda wani barawo ya gamu da fushin wani tafkeken maciji.

Legit.ng dai ta samu cewa lamarin dai ya auku ne a kauyen Kyenjojo da ke a shiyyyar yammacin kasar ta Uganda.

Yadda lamarin ya auku dai kamar yadda muka samu shine, jim kadan bayan wani kasurgumin barawo ya shiga wani gida inda ya saci katifa ya kuma yi niyyar guduwa, sai kawai maciji ya kama shi.

Shaidun gani da ido dai sun bayyana cewa macijin ya sulalo ne inda kuma ya rataye barawon ta wuyan sa duk da cewa bai cutar da shi ba ta hanyar sari.

Hakan ne dai ya sanya barawon kuka sosai tare da yadda katifar da ya sato wanda jin kukan na sa ne ma ya sa al'ummar yankin suka zo wurin sa domin ganin me ke faruwa tare da kai masa dauki.

Daga karshe dai kamar yadda muka samu, barawon ya samu taimako daga al'ummar inda aka kira wani mai wasa da maciji ya kore shi.

A wani labarin kuma, Wata kotu a garin Abuja, babban birnin tarayya mun samu cewa ta aikewa da shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma Sanatan dake wakiltar wata mazaba a jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki da sammaci game da fashin bankunan garin Offa.

Kotun dai wadda ke da matsayi na daya tana zaman ta ne a unguwar Lugbe a garin na Abuja kuma ta umurci shugaban jami'an 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris da ya kamomata shugaban majalisar dattawan ya kuma gurfana a gaban ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel