Cakwakiya: Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa

Cakwakiya: Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa

- Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa

- Tace dole ne ya zo ya kare kan sa

- Wani dan kishin kasa ne ya shigar da karar kotun

Wata kotu a garin Abuja, babban birnin tarayya mun samu cewa ta aikewa da shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma Sanatan dake wakiltar wata mazaba a jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki da sammaci game da fashin bankunan garin Offa.

Cakwakiya: Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa

Cakwakiya: Wata kotu ta aikewa da Bukola Saraki sammaci game da fashin bankunan Offa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An kama wani dan siyasar Najeriya yana wanka tsirara

Kotun dai wadda ke da matsayi na daya tana zaman ta ne a unguwar Lugbe a garin na Abuja kuma ta umurci shugaban jami'an 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris da ya kamomata shugaban majalisar dattawan ya kuma gurfana a gaban ta.

Legit.ng ta samu cewa wannan umurnin na kotun dai ya biyo bayan wata kara da wani dan kishin kasa Mista Oluwatosin Ojaomo ya shigar inda ya bukaci kotun da ta kira Sarakin domin ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa.

Idan dai mai karatu bai manta ba a kwanan baya ne dai wasu matasa suka yi fashi a bankuna da dama a garin Offa dake a jihar Kwara, inda kuma bayan an kama su suka bayyana cewa Bukola Saraki yana taimaka masu.

A wani labarin kuma, Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel