Daga karshe: Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati

Daga karshe: Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati

- Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati

- Korar da Buhari yayi mu ni gaba ta kai ni ma - Babachir Lawal

- Yace shi tuni ya manta da batun

A wani yanayi dake zaman karon farko tun bayan korar sa daga mukamin sa na babban Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya da Shugaba Buhari yayi a watannin baya, Injiniya Babachir Lawal yayi magana da 'yan jarida a karon farko.

Daga karshe: Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati

Daga karshe: Babachir Lawal yayi magana karon farko bayan korar sa daga gwamnati
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dan luwadi ya zayyana wasu kanciya da shi a Najeriya

Shi dai tsohon Sakaten gwamnatin tarayyar, ya bayyana cewa ko kusa shi korar da Shugaba Buhari yayi masa daga gwamnatin sa a watannin baya ma shi gaba ta kai shi.

Legit.ng ta samu cewa Babachir yayi wannan ikirarin ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Haka zalika Babachir yace shi tuni ya ma ajiye maganar a bayan sa ya kuma cigaba da harkokin kasuwanci da kuma noman sa da dama can da su ne ya dogara kafin shigar sa gwamnati.

"Sadda ina Sakataren gwamnati duka-duka albashi na Naira dubu dari 930 ne a duk wata wanda daman can bai isa ta amma yanzu na koma kasuwaci na da noman da nike yi".

A don haka ne ma Babachir din ya bayyana cewa shi korar da akayi masa ma gaba ta kaishi wai gobarar titi a Jos.

A wani labarin kuma, Mataimakin kakakin majalisar wakilai a tarayyar Najeriya mai suna Honorabuk Yussuf Lasun a ranar Lahadin da ta gabata ya fito karara ya bayyanawa duniya shi har yanzu yana nan jam'iyyar sa ta All progressives Congress (APC).

Wannan dai kamar yadda muka samu, na zaman tamkar martani ga labaran da suka yi ta yawo a kwanakin baya na cewa mataimakin kakakin majalisar ta tarayya ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel