Adeosun ta kawo tsarin TSA, VAIDS a lokacin da ta ke aiki a Gwamnatin Tarayya

Adeosun ta kawo tsarin TSA, VAIDS a lokacin da ta ke aiki a Gwamnatin Tarayya

A makon jiya ne zargin da ke kan Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun na laifin badakalar takardar shaidar kammala bautar kasa watau NYSC ya ci ta har ta kai ga yin murabus daga matsayin ta a Gwamnatin Buhari.

Adeosun ta kawo tsarin TSA, VAIDS a lokacin da ta ke aiki a Gwamnatin Tarayya

Kemi Adeosun ta kawowa Gwamnatin Buhari tsare-tsare masu amfani
Source: UGC

Yanzu haka mun kawo wasu gyare-gyare da tsohuwar Ministar kudin ta kawo a bangaren tattalin arziki da za a dade ba a manta da ita ba. Daga cikin wadannan gyare-gyare akwai:

1. TSA

Tsohuwar Ministar kudin ce tayi kokari wajen dabbaka tsarin nan na asusun bai-daya watau TSA wanda yayi wa Najeriya rana inda kasar ta tara sama da Tiriliyan 7 daga farkon Gwamnatin Buhari zuwa yanzu.

2. VAIDS

Ministar ta kawo wani tsari na karbar haraji daga hannun Jama’a ta lalama. A sanadiyyar haka dai Adeosun ta tarawa Najeriya kudin shiga ta hanyar haraji. Yanzu masu biyan haraji a kasar sun kusa kai miliyan 20.

KU KARANTA: Adeosun ta sulale ta bar Najeriya bayan tayi murabus

3. Whistle blower

Kemi Adeosun ta kawo wani tsari na “Whistle blower” wanda zai bada dama mutum ya samu rabon sa idan ya tona asirin wadanda su ka tafka sata a kasar. Hakan ya sa aka rika gano kudin sata ana maidawa Gwamnati.

Bayan wadannan dai akwai kokarin da Ministar da tayi murabus tayi wa Gwamnatin Buhari wajen adana kudi. Ministar ta kirkiro wani bangare a Ma’aikatar ta da ta sa Jami’an Gwamnati su ka rage fatali da kudi wajen zirga-zirga da taro iri-iri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel