Zamu kashe Leah Sharibu nan da wata guda – Boko Haram sunyi barazana ga gwamnatin tarayya

Zamu kashe Leah Sharibu nan da wata guda – Boko Haram sunyi barazana ga gwamnatin tarayya

Kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun yi barazanar kashe Leah Sharibu, yan makarantar Dapci dake jihar Yobe guda daya tilo da ta saura a hannunsu cikin 119 da aka sace a watan Fabrairu.

Barazanar na zuwa ne yayinda gamayyar kungiyar Boko Haram suka kashe Saifura Ahmed, daya daga cikin ma’aikatan agaji uku da aka sace a Rann, karamar hukumar Kala Balge.

A cewar shafin The Cable, an sace Ahmed ne a lokaci wata mamaya da aka kai sansanin soji a yankin a ranar 1 ga watan Maris.

Akalla sojoji hudu, jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar agaji uku aka kashe a harin.

Zamu kashe Leah Sharibu nan da wata guda – Boko Haram sunyi barazana ga gwamnatin tarayya

Zamu kashe Leah Sharibu nan da wata guda – Boko Haram sunyi barazana ga gwamnatin tarayya
Source: Depositphotos

Hauwa Leman, daya daga cikin ma’aikatan da aka sace ta aikawa daya daga cikin kawayenta sakon murya ida ta bukaci ta fadama iyayenta cewar an kamata.

KU KARANTA KUMA: Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo

Yan ta’addan sun yi ikirarin cewa sun tuntubi gwamnati akan kamunamma babu wani bayani.

“Mun tuntubi gwamnati ta hanyar rubutu sannan kuma mun aike da sakonin murya amma gwamnati tayi watsi damu. Don haka ga sakon jini,” inji kakakin kungiyar wanda bai bayyana sunansa ba.

“Sauran malamar jinya da mai karban haihuwa da zamu hukunta kamar haka a wata daya mai zuwa, harda Leah Sharibu.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel