2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan takara – Balarabe Musa

2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan takara – Balarabe Musa

Gabannin zaben 2019, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigon kungiyar dattawan arewa, Balarabe Musa ya yi duba sosai ga harkokin kasar sannan ya bayyana cewa koda dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa ýan Najeriya tun bayan zabarsa a 2015, babu dan takara ko daya daga jam’iyyun adawa da ya shirya kai Najeriya inda take mafarkin kaiwa.

Tsohon gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba yace tulin yan takaran dake neman shugabanci a yanzu babu wadda ya nuna cewa zai sanya ci gaba al’umma sama da son zuciyarsa.

A cewarsa, kasar na bukatar ingantaccen shugaba a 2019 wadda zai hada kan kabilun kasar, yayi amfani da samunta wajen yiwa mutane aiki sannan ya kawo karshen cin hanci da rashawa a manyan wurare.

2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan takara – Balarabe Musa

2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan takara – Balarabe Musa
Source: Depositphotos

Ya kuma koka akan tsarin shiga lamarin siyasa a kasar, cewa tsadar abun shi ya hana wadanda ke son kawo ci gaba fitowa tsanin siyasar kasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba ya bukaci ýan Najeriya da kada su nuna kabilanci wajen zabar shugabanni kawai abunda zasu duba shine hangen nesan shugaba wajen kawo chanji.

KU KARANTA KUMA: Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo

Saraki dan takaarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan a Lagas yayinda yake jawabi ga mambobin jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ziyarar da ya kai sakatarioyar jam’iyyar na daga cikin rangajin da yake na neman goyon baya akan kudirinsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel