Kuma dai, gwamnan jihar Akwa Ibom ya sake babban rashi

Kuma dai, gwamnan jihar Akwa Ibom ya sake babban rashi

Wani babban hadimin gwamnan jihar akwa Ibom Udom Emmanuel, ya yi murabus daga kujerarsa a gidan gwamnan jihar.

Hadimin mai suna Aniete Ebe wanda ya kasance hadimi na musamman kan sanya hannun jari da masana’antu ya kasance yana aiki da ofishin masu sanya hannun jari daga kasashen waje a birnin jihar, Uyo.

Ebe ya bayyanawa gwamnan niyyar murabus dinsa ne bisa ga rashin bashi makamashin aiki da alfanu tun lokacin da aka nada shi a shekarar 2015.

Kana Ebe wanda ‘dan tsohon mataimakin gwamnan jihar, Valerie Ebe, ya laburtawa gwamnan cewa ya sauya sheka daga daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Wannan matashi ya bi sawun mahaifiyarsa Mrs Ebe wacce ta sauya sheka zuwa APC a kwanakin baya.

KU KARANTA: Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari

Ebe ya bayyanawa maenma labarai ranan Litinin cewa shi da ma’aikatansa basu taba zuwa wannan faggen aiki ba tun lokacin da aka nada su shekaru uku yanzu.

Yace: “Wasu hadiman da yawa suna niyyar murabus. Abinda ke rike kawai shine albashin da suke samu. Amma zuwa karshen wannan gwamnati za su bari.

Da yawansu sun tsaya ne saboda albashi, kun san yadda abubuwa sukayi wuya.”

Ya bayyana cewa jihar Akwa Ibom na bukatar shugaba mai cika alkawari ba wanda zai rika shugabanci tamkar shugabancin ofishin kansa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel