Cikin hotuna: Jihar Akwa Ibom ta fara Buhariyya yayinda tawagar manyan jihar suka kawo ziyara

Cikin hotuna: Jihar Akwa Ibom ta fara Buhariyya yayinda tawagar manyan jihar suka kawo ziyara

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawagar manyan jihar Akwa Ibom, a fadar shugaban kasa Aso Villa a yau Litinin, 17 ga watan Satumba, 2018.

Tawagar manyan jihar ya kunshi tsohon shugabana maras rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Atuekong Don Etiebet, Senator John Akpan Udoedehe, Umana Okon Umana da Senator Aloysius Etok.

Cikin hotuna: Jihar Akwa Ibom ta fara Buhariyya yayinda tawagar manyan jihar suka kawo ziyara

Cikin hotuna: Jihar Akwa Ibom ta fara Buhariyya yayinda tawagar manyan jihar suka kawo ziyara
Source: Facebook

Jihar Akwa Ibom na daga cikin jihohin da za'a sha kallo a zaben 2019 saboda irin yadda siyasar jihar ta canza tsakanin zaben 2015 zuwa yanzu.

Wannan ya biyo bayan sauya shekar babban jigon jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Godswill Akpabio, kwamishana, da kuma babban hadimin gwamnan jihar.

A karshen makon da ya gabata, matasa mabiya addinin Kirista na jihar Akwa Ibom sun shirya taron addu'a na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel