Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo

Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo

- Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar

- Ya ce zai cimma wannan manufa ne idan har yan Najeriya suka basa dama ta hanyar zabarsa

- Gwamnan yayi jaje ga wadanda harin kauyukan Gon, Nzumosu, Bolki, Nyanga da Bukuto dake karamar hukumar Numan na jihar Adamawa ya cika dasu

Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo

Zan kawo karshen kashe-kashen kabilanci da na addini idan na zama shugaban kasa - Dankwambo
Source: Twitter

Gwamnan yayi jaje ga wadanda harin kauyukan Gon, Nzumosu, Bolki, Nyanga da Bukuto dake karamar hukumar Numan na jihar Adamawa ya cika dasu, inda aka kashe malami da wasu mutane 51.

KU KARANTA KUMA: Lokacin yayi da yan yankin Arewa ta Tsakiya za su yi shugabancin Najeriya – Saraki

Ya bayyana cewa idan har aka bashi damar shugabancin Najeriya a 2019, zai yi amfani da tsarin da yake amfani dashi wajen tsaron Gombe a fadin kasar.

Legit.ng ta rahoto cewa Dankwambo yace zai samar da mafita ga kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta idan zabe shi a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel