Da duminsa: Hukumar NEMA ta lissafa jihohi 4 da mummunar ambaliyar ruwa ke yiwa barazana

Da duminsa: Hukumar NEMA ta lissafa jihohi 4 da mummunar ambaliyar ruwa ke yiwa barazana

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Mustapha Maihaja, ya bayyana ambaliyar ruwan damina, da ake fuskanta a sassan Najeriya, a matsayin annoba a wasu jihohi hudu.

Jihohin da Maihaja ya ce ambaliyar ruwan ta zama annoba sune; Kogi, Niger, Delta da Anambra.

Kazalika, NEMA ta lissafa wasu jihohi 8 da zata matukar saka idanu kansu saboda barazanar da ambaliya ke yi masu.

Ko a labaran Legit.ng na ranar yau, Litinin, kun ji cewar tun kafin fara saukar ruwan sama hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) tayi hasashen za a samu ambaliyar ruwa a daminar bana. Sai dai hukumar ba ta fadi yankin da ambaliyar zata fi shafa ba.

Da duminsa: Hukumar NEMA ta lissafa jihohi 4 da mummunar ambaliyar ruwa ke yiwa barazana

Ambaliyar ruwa
Source: Twitter

A yanzu haka jihohin Najeriya, a kudu da arewa, na fuskantar annobar ambaliyar ruwa dake cigaba da haifar da asarar rayukan mutane, dabbobi da dumbin dukiya.

DUBA WANNAN: A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin jiragen yaki 30

Gwamnatin Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 31, lalata gidaje fiye da 10,000 da fiye da hekta 5000 na gonaki sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye garuruwa da dama a kananan hukumomi 20 na jihar.

Sai dai wasu alkaluma da ba na gwamnati ba sun bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu ya haura hakan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel