Bafarawa ya ziyarci Afenifere, ya yi alkawarin cika musu alkawarin da Osinbajo ya gaza

Bafarawa ya ziyarci Afenifere, ya yi alkawarin cika musu alkawarin da Osinbajo ya gaza

- Daya daga masu neman takarar a PDP, Attahiru Bafarawa ya yi alkawarin canja tsarin rabon arzikin kasa idan ya zama shugaban kasa

- Bafarawa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya ziyarci 'yan kungiyar Afenifere da a garin Akure

- Bafarawa ya ce yin garambawul ga tsarin rabon arzikin kasa ne kawai zai magance matsalolin da ke adabar Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa a PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya yi alkawarin canja tsarin rabon arzikin kasa idan aka zabe shi shugaban kasa a 2019.

Bafarawa ya ziyarci Afenifere, ya yi alkawarin cika musu alkawarin da Osinbajo ya gaza

Bafarawa ya ziyarci Afenifere, ya yi alkawarin cika musu alkawarin da Osinbajo ya gaza
Source: Depositphotos

Bafarawa ya yi wannan alkawarin ne yau Litinin a garin Akure, yayin da ya kai ziyara ga kungiyar Yarabawa ta Afenifere, ya ce baya ga goyon bayan sauyin tsarin rabon arzikin kasa da ya ke yi, ya yi alkawarin zartas da canjin mudin aka zabe shi shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa (Bidiyo)

Ya ce yin garambawul ga tsarin rabon arzikin kasa ne kawai zai magance matsalolin da suke adabar Najeriya tare da kawo hadin kai mai dorewa a kasar.

Tsohon gwamnan ya ce duk wanda ke maganar canja tsarin rabon arzikin kasa yana nufin kawo cigaba ne a Najeriya ba wai magana ya ke domin ra'ayin siyasa ko bangaranci ba.

"Za muyi aiki tare da majalisar tarayya da sashin shari'a domin duba shawarwarin da aka bayar a tarukan yiwa kasa garambawul domin mu duba yadda zamu biya wa al'umman Najeriya bukatunsu," Inji Bafarawa.

Kazalika, ya ce idan ya zama shugaban kasa ba zai bata lokaci wajen ramuwar gayya ba saboda idan aka cigaba da hakan ba za'a samu wani cigaba mai ma'ana a kasar ba, sai dai zai mayar da hankali wajen ayyukan more rayuwa ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel