Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN

- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirye-shiryen da take yi na daukar yan Najeriya marasa aiki guda 5,000

- Zata dauke su aiki ne a shirin BRISIN

- Shirin wani tsari ne na karba, tattara da rarraba bayanai domin tallafawa hukumar tattalin arziki

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirye-shiryen da take yi na daukar yan Najeriya marasa aiki guda 5,000 a babban birnin tarayya karkashin shirin Basic Registry and Information System in Nigeria (BRISIN).

Dr Anthony Uwa, shugaban shirin na BRISIN a Najeriya ya fadawa manema labarai hakan a ranar Lahadi, 16 ga watan Satumba a Abuja cewa za’a dauki yan Najeriya da dama bayan shirin farko.

Shirin BRISIN wani tsari ne na karba, tattara da rarraba bayanai domin tallafawa hukumar tattalin arziki.

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN
Source: Depositphotos

Uwa yace tsarin ya ta’allaka ne wajen kawo ci gaba da habbakan tattalin arzikin kasar ta hanyar amfani da bayanan mutane da sauran bayanai makamantan hakan.

NAN ta ruwaito cewa an kafa shirin ne a gwamnatin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, yayinda gwamnatin Goodluck Jonathan ta kaddamar da kwamitin kimiya don shirin nata.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi

Uwa ya bayyana cewa shirin zai kassance a fanni daban-daban inda za a tura wadanda suka yi nasarar shiga shirin kasar Italy domin a basu horo.

Sannan daga bisani za’a dauki Karin ma’aikata bayan 5,000 din farko.

Ya kuma bayyana cewa za’a bude shafin yanar gizo da mutun zai yi amfani das hi wajen shiga shirin a mako mai zuwa, kuma kwashe makonni shida a bude.

Ya kuma bayyana cewa wannan shiri baida nasaba da siyasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel