Lokacin yayi da yan yankin Arewa ta Tsakiya za su yi shugabancin Najeriya – Saraki

Lokacin yayi da yan yankin Arewa ta Tsakiya za su yi shugabancin Najeriya – Saraki

Shugaban majalisar dattawa n Najeriya kuma dan takarar kujean shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa lokaci yayi da dan yankin Arewa ta Tsakiya zai zamo shugaban kasar Najeriya.

Saraki ya bayyana hakan ne a garin Jos, babban birnin jihar Plateau a wajen wani taro na wakilan jam’iyyar PDP a jihar.

Shugaban majalisar na cewa: “Mu ‘yan jihohin Kwara, Filato, Benuwai, Kogi da Nasarawa mun bauta wa kasar nan matuka sannan duk hadin kan mu yanzu mun samu rabuwar kai sosai. Dole mu dawo mu dinke tamau domin samun wannan dama.

Lokacin yayi da yan yankin Arewa ta Tsakiya za su yi shugabancin Najeriya – Saraki

Lokacin yayi da yan yankin Arewa ta Tsakiya za su yi shugabancin Najeriya – Saraki
Source: Depositphotos

“Muna bukatar shugaban kasan da zai ja kowa a jika, Wanda kowa na shi ne, wanda duk ‘yan Najeriya na sa ne kuma ya dauki kowa daya.

“Lokacin mu yayi yanzu, dole mu canza tsarin mulki a kasar nan mu karkato da akalar zuwa wannan yanki . Dole ‘yan Najeriya su hada karfi da karfe domin ceto Najeriya daga halin da ta shiga.

Saraki ya kara da cewa shi shugaba ne mai adalci, kishi da sanin ya kamata, cewa kowa ya ga yadda ya ke shugabantar majalisar dattawa ba tare da nuna bambanci ba

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar kuma tallata hajoji a jihar Kwara tayi barazanar cire allunan tallar duk wani dan siyasa a jihar da bai biya kudaden haraji ga hukumar ba.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi

Shugaban hukumar, Ahmed Olufadi, ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Litinin, a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Sai dai wasu magoya bayan jam’iyyar APC sun ce gwamnatin jihar na son fakewa da sunan haraji domin hana ‘yan takaarar ta kafa fastoci da tallata kansu a manyan biranen jihar. Sai dai Olufadi ya bayyana cewar fiye da kashi 90 na allunan tallar ‘yan siyasa a jihar ba bisa ka’ida da doka aka kafa su ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel