Wata jihar PDP a arewa zata cire allunan tallar ‘yan takarar APC

Wata jihar PDP a arewa zata cire allunan tallar ‘yan takarar APC

- Hukumar kuma tallata hajoji a jihar Kwara tayi barazanar cire allunan tallar duk wani dan siyasa a jihar da bai biya kudaden haraji ga hukumar ba

- Magoya bayan jam’iyyar APC sun ce gwamnatin jihar na son fakewa da sunan haraji domin hana ‘yan takaarar ta kafa fastoci da tallata kansu

- Sai dai shugaban hukumar, Olufadi, ya bayyana cewar fiye da kashi 90 na allunan tallar ‘yan siyasa a jihar ba bisa ka’ida da doka aka kafa su ba

Hukumar kuma tallata hajoji a jihar Kwara tayi barazanar cire allunan tallar duk wani dan siyasa a jihar da bai biya kudaden haraji ga hukumar ba.

Shugaban hukumar, Ahmed Olufadi, ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Litinin, a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Sai dai wasu magoya bayan jam’iyyar APC sun ce gwamnatin jihar na son fakewa da sunan haraji domin hana ‘yan takaarar ta kafa fastoci da tallata kansu a manyan biranen jihar.

Sai dai Olufadi ya bayyana cewar fiye da kashi 90 na allunan tallar ‘yan siyasa a jihar ba bisa ka’ida da doka aka kafa su ba.

Wata jihar PDP a arewa zata cire allunan tallar ‘yan takarar APC

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed
Source: Depositphotos

Da yawan allunan tallar ‘yan siyasar dake son yin takara a zaben 2019 ba bisa ka’ida da doka aka kafa su a sassan jihar Kwara ba. Kullum sai mun farka mun ga sabbin fastocin a manyan titunan mu, musamman a birnin Ilorin, wannan rashin tsari ne da girmama doka, hakan ne ma ya sa sai dare ake lika fastocin ko kafa allunan,” a cewar Olufadi.

Yanzu haka dai Olufadi ya bawa dukkan ‘yan siyasa wa’adin mako guda ga ‘yan siyasar da aka kafa allunan tallarsu ko fastoci ba tare da biyan hukumar kudin haraji ba, da su cire su da kansu don gujewa fushin hukuma.

DUBA WANNAN: Annoba: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 31, ta rushe gidaje fiye da 10,000 a Kano

Olufadi y ace hukumar sa zata hada kai das ashen tsaro na fadin kaya (DSS) domin cire allunan duk dan takarar da bai biya hukumar ba bayan karewar wa’adin day a diba masu.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya koma jam'iyyar PDP tare da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a watan da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel