Tawagar shahararren dan sanda Abba Kyari sunyi gagarumin nasara

Tawagar shahararren dan sanda Abba Kyari sunyi gagarumin nasara

- Shahararren jami'in dan sandan nan Abba Kyari ya cafke wani babban dan ta'adda

- Dan ta'addan ya kasance daya daga cikin masu laifin da ake nema ruwa a jallo

- Abba Kyari ne ya sanar da hakan a shafinsa na zumunta

Tawagar shahararren dan sandan nan, Abba Kyari sunyi nasarar cafke daya daga cikin yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a kasar.

Babban jami’in dan sandan ne ya bayyana wannan gagarumin nasara da suka samu a shafinsa na Facebook, a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Ya rububuta a shafinsa: “Ina matukar farin ciki a yau, yanzun nan na samu wani babban nasara wajen yaki da laifi. Na kama daya daga cikin manyan masu laifi kuma dan ta’addan da ake nema ruwa a jallo a kasar. Kakakin rundunar yan sandan zai sanar da hakan sannan ya bayar da cikakken bayani nan bada jimawa ba.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Lamido ya gurfana a gaban shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya

Tawagar shahararren dan sanda Abba Kyari sunyi gagarumin nasara

Tawagar shahararren dan sanda Abba Kyari sunyi gagarumin nasara
Source: Facebook

A wani lamari makamancin haka, hukumar sojin sama ta kasa ta bayyana cewar ta samu karin jiragen yaki domin kara karfafa yaki da aiyukan ta'addanci.

A cewar hukumar sojin sama, ta samu karin jiragen yaki 30 cikin wata 18 da suka wuce tare da bayyana cewar tuni ta fara amfani da 13 daga adadin jiragen a kokarinta na gani ta kara zage dantse wajen tabbatar da tsaron kasa.

Shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Sadique Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya, Lahadi, yayin bikin bude sabuwar shelkwatar horon sojojin sama a Kaduna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel