Annoba: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 31 tare da rushe gidaje fiye da 10,000 a Kano

Annoba: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 31 tare da rushe gidaje fiye da 10,000 a Kano

- Hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) tayi hasashen cewar za a samu ambaliyar ruwa a daminar bana

- Yanzu haka jihohin Najeriya da daman a fuskantar annobar ambaliyar da ta haifar da asarar rayukan mutane, dabbobi da dukiya

- Ambaliayar ruwa a jihar Kano tayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 31 da asarar dukiya da ta zarta miliyan dubu (biliyan) biyar

Tun kafin fara saukar ruwan sama hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) tayi has ashen za a samu ambaliyar ruwa a daminar bana. Sai dai hukumar ba ta fadi yankin da ambaliyar zata fi shafa ba.

A yanzu haka jihohin Najeriya, a kudu da arewa, na fuskantar annobar ambaliyar ruwa dake cigaba da haifar da asarar rayukan mutane, dabbobi da dumbin dukiya.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 31, lalata gidaje fiye da 10,000 da fiye da hekta 5000 na gonaki sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye garuruwa da dama a kananan hukumomi 20 na jihar.

Sai dai wasu alkaluma da ba na gwamnati ba sun bayyana cewar adadin mutanen da suka mutu ya haura hakan.

Annoba: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 31 tare da rushe gidaje fiye da 10,000 a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Alhaji Aliyu Bashir, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano (SERERA), ya ce bayan asarar rayukan mutane 31, ambaliyar ruwan ta lalata gidaje, gonaki da dukiyar da yawanta ya kai biliyan N5bn.

Kazalika ya bayyana cewar annobar ambaliyar rowan ta shafi a kalla manoman jihar 35,000 a fadin kananan hukumomi 8.

Kayan amfanin gonad a ambaliyar ta fi yiwa illa akwai masara, auduga, farin wake, albasa, shinkafa, gyada, gero da ragowar amfanin gona masu kwaya.

DUBA WANNAN: A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin jiragen yaki 30

Bashir ya yi alkawarin cewar nan bada dadewa ba hukumar SERERA zata fitar da cikakken rahoto a kan annobar domin mikawa gwamnatin jiha don sanin matakin da zata dauka.

Yanzu haka mazauna kauyukan da ambaliyar ta fi muni sun koma kwana a makarantun gwamnati tare da amfani da kwale-kwale domin fita ko shiga wasu kauyukan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel