Yanzu Yanzu: Lamido ya gurfana a gaban shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya

Yanzu Yanzu: Lamido ya gurfana a gaban shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya

Shugabanni daga yankuna hu daga cikin shida na kasar, karkashin kungiyar shugabannin kudu da arewa ta tsakiya na cikin tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Sule Lamido.

Shugabannin karkashin jagorancin tsohon kwamishinan bayanai na tarayya kuma shugaban kudu maso kudu, Cif Edwin Clark suna jefa masa tabayoti kan tanadin da yake yiwa Najeriya gabannin zaben shugaban kasa na 2019.

Tsohon gwamnan jihar Jigawan ya gurfana a gaban kungiyar a ranarLitinin, 17 ga watan Satumba a gidan Clark dke Asokor, Abuja domin amsa tambayoyi, musamman akan sake fasalin lamuran kasar wadda kungiyar ke kokarin ganin anyi.

Yanzu Yanzu: Lamido ya gurfana a gaban shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya

Yanzu Yanzu: Lamido ya gurfana a gaban shugabannin Kudu da Arewa ta tsakiya
Source: Depositphotos

Haka zalika kungiyar na son sanin shirye-shiryensa wajen habbaka tattalin arziki daga durkushewa da kuma kawo ci gaba a kasar.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau

Kafin shirin tambayoyi da amsan, Cif Clark ya fada masa cea ungiyar bazata tsayar da kowani dan takara ba har sai ta ba dukkansu damar jin ta bakinsu harda Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Zuwa yanzu dai yan takara hudu ne suka bayana a gaban kungiyar a gidan Cif Clark dake Abuja.

Sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, Sina Fagbenro na jam’iyyar KOWA da kuma Lamido.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel