Da duminsa: Majalisa ta fara gyaran dokar zabe da Buhari ya yi watsi da ita sau 2

Da duminsa: Majalisa ta fara gyaran dokar zabe da Buhari ya yi watsi da ita sau 2

- Majalisa ta fara zama domin sake duba dokar zabe da shugaba Buhari ya yi watsi da ita a baya

- Shugaba Buhari ya ki amincewa da dokar gyaran zaben ne saboda wasu kurakurai da ke ciki

- Kwamitin gyarar dokar zaben ta ce za tayi iya kokarinta domin ganin dokar ta samu amincewa

Majalisar tarayya ta fara aikin kan kudirin yin garambawul ga dokar zabe na 2010 da shugaba Muhammadu Buhari ya ki saka hannu a kai saboda wasu matsaloli da ya ke son majalisar ta gyra.

Mambobin majalisar dattawa da na wakilai na kwamitin gyarar dokar zaben ne suka bayar da sanarwan a yau Litinin a Abuja inda suka ce kwamitin ta fara zama domin duba dalilan da yasa shugaba Buhari ya ki amincewa da kudirin domin su gyara.

Da duminsa: Majalisa ta fara gyaran dokar zabe da Buhari ya yi watsi da ita sau 3

Da duminsa: Majalisa ta fara gyaran dokar zabe da Buhari ya yi watsi da ita sau 3
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

A lokacin da ya ke magana da manema labarai kafin kwamitin ta shiga taron ta, Ciyaman din kwamitin INEC a majalisa, Sanata Suleiman Nazifi ya ce kwamitin na da babban nauyi a kanta saboda dukkan 'yan Najeriya sun sanya musu ido.

Nazif ya kuma ce wannan shine karo na hudu kwamitin za tayi aiki kan kudirin dokan wanda shugaba Buhari ya mayarwa majalisar har sau biyu.

"Nayi imanin cewa aikin da mu keyi zai amfani 'yan Najeriya, Inji Nazif.

Shugaba Buhari ya aike wasika ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara domin sanar da matsayarsa na kin amincewa da dokar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel