Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Matafiya da ke bin titin Abuja zuwa Lokoja sun kwashe sa'o'i masu yawa saboda zanga-zanga da dirbobin tanka su keyi wanda hakan yasa suka kulle babban titin da ke Jamata.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da tawagarsa yana daya daga cikin wanda suka kwashe sa'o'i a titin a hanyarsa ta zuwa Abuja domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa.

A cewar, Akinti Onyegbule, sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kogi, direbobin tankan sun fara zanga-zangan ne bayan wani soja ya harbi tayoyin wata tanka.

Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Ya ce gwamnan ya kwashe kusan sa'a guda yana sulhu kafin masu zanga-zangan suka hakura suka janye motocinsu daga titin.

Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari

Masu zanga-zanga sun bata lokacin wani gwamna a hanyarsa ta zuwa wurin Buhari
Source: Twitter

"A safiyar yau, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gamu da wasu direbobin tanka masu zanga-zanga a babban titin Abuja zuwa Lokoja da suka rufe hanyar saboda wani soja ya harbi tayan wata tanka.

"Gwamna Yahaya Bello ya kwashe fiye da sa'a guda a titin yana kokarin sulhunta bangarorin biyu kafin daga baya aka bude hanyar.

"Gwaman ya yi kira ga masu ababen hawa da jami'an tsaro su rika fahimtar juna tare da yin sulhu cikin ruwan sanyi ba tare da jefa saura direbobi cikin wahala ba," inji Onyegbule.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel