A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin sabbin jiragen yaki 30

A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin sabbin jiragen yaki 30

Hukumar sojin sama ta kasa ta bayyana cewar ta samu karin jiragen yaki domin kara karfafa yaki da aiyukan ta'addanci.

A cewar hukumar sojin sama, ta samu karin jiragen yaki 30 cikin wata 18 da suka wuce tare da bayyana cewar tuni ta fara amfani da 13 daga adadin jiragen a kokarinta na gani ta kara zage dantse wajen tabbatar da tsaron kasa.

Shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Air Marshal Sadique Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya, Lahadi, yayin bikin bude sabuwar shelkwatar horon sojojin sama a Kaduna.

A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin sabbin jiragen yaki 30

A kori ta'addanci: Hukumar sojin sama ta samu karin sabbin jiragen yaki 30
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Bayan yaki da ta'addanci, jiragen zasu yi amfani wajen kara horar da sojojin sama a bangaren sarrafa jiragen yaki, musamman a yanayi na yaki.

Ya kara da cewar hukumar soji na kokarin kara karfin rundunarta ta hanyar daukan sabbin ma'aikata 1,500 duk shekara.

Sadique ya ce hukumar sojin sama zata cigaba tare da kara kaimi a bangaren inganta rayuwar jami'anta tare da kula da jin dadinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel