Yadda wasu gaggan yan damfara ke tafka tsiyarsu daga cikin Kurkuku Kuje

Yadda wasu gaggan yan damfara ke tafka tsiyarsu daga cikin Kurkuku Kuje

Dubun wasu yan damfara macuta wadanda suke shirya tsiyarsu daga gidan kurkuku ta cika bayan sun fada hannun jajirtaccen dansandannan, shugaban yansanda na musamman dake karkashin umarnin babban sufetan Yansanda, Abba Kyari.

Asirin yan damfarar ta cika ne bayan sun damfari wani dan kasuwa mai sayar da motoci mai suna Ige Olaleye a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2017 a kamfanin Elizade Motors, inda ya nemi a bashi motoci guda uku akan kudi naira miliyan 38.9.

KU KARANTA: Shamsuna Ahmad ta kama aiki gdan gadan a matsayin sabuwar ministar kudi

Legit.ng ta ruwaito wani daga cikin yan damfarar mai suna Dalhatu Yahaya ne ya isa wannan kamfani, inda ya nemi su bashi motoci uku da suka hada da Toyota Hilux, Toyota Prado da kuma Toyota Land cruiser.

Yadda wasu gaggan yan damfara ke tafka tsiyarsu daga cikin Kurkuku Kuje

Yan damfarar

Bayan Olaleye ya bashi takardar farashin motocin sai Dalhatu ya tafi da nufin zai turo musu kudade daga bisani kuma su je su dauki motocin, daga nan ciniki ya kaya, ashe basu san Dalhatu yana aiki ne tare da wani Maigidansa ifeanyi Ezenwa dake garkame a Kurkukun Kuje.

Olaleye yace: “Babban dan damfarar shine Ezenwa kuma yana daure ne a kurkukun Kuje, amma yana amfani da Yahaya wajen damfarar mutane, a lokacin da na bukaci na san wanene maigidan Yahaya daya aikoshi sayan motoci sai nan take ya kira wani mutumi a waya, yace mana shine magidansa.

“Asali ma Maigidan Yahaya ya bayyana mana sunansa a matsayin Dakta Sam Attah, kuma yace mana shi mazaunin jahar Legas ne, don haka ya bukaci mu baiwa Yahaya farashin motocin daya bukata, daga nan tafi bamu kara jin duriyarsu ba.” Inji Olaleye.

Bayan wasu yan kwanaki sai Yahaya ya kira Olaleye a waya yana cewa sun sanya naira miliyan talatin da takwas da dubu dari takwas a asusun bankin kamfanin, daga nan sai Olaleye ya bukaci Yahaya ya turo masa takardar shaidar biyan kudin, kuma ya tura masa, daga nan ma’aikatan kudi na kamfanin suka tabbatar da shigar kudin.

Sai dai koda Yahaya yaje daukan motocin sai ya tarar daya ne kawai da akwai a kamfanin, anan suka bashi motar hilux suka rokeshi ya dawo bayan wani lokaci don daukan sauran motocin, kuma Yahaya ya yarda, harma yace a rubuta sunan wata Eniola Oladapo Hannah akan rasidin.

Bayan kwanaki biyu sai shugaban yan damfarar ya kira kamfanin motocin yace a ninka adadin motocin da suka nema, kuma zai turo kudaden, aikuwa bayan wasu yan kwanaki sai ya sake turo kudi naira miliyan 39.8.

Amma bayan kwanaki sai jami’in kudi na kamfanin yana bayyana musu cewa tuni an kwashe kudaden da aka zuba a asusun bankin nasu, kuma duk kokarin da suka yi na gano mutanen yaci tura, daga nan ne suka mika kara ka hukumomin EFCC, ICPC da kuma yansandan IRT na Abba Kyari.

Abinka da rabo, yayin da yansanda ke farautar mutanen nan, kwatsam sai shugabansu daga gidan yarin ya kirasu yana bayyana musu inda Yahaya yake boye, sakamakon Yahaya ya arce da motocin da suka damfara, inda kuma ba tare da bata lokaci ba Yansanda suka kama Yahaya da motar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel