Shamsuna Ahmad ta kama aiki gdan gadan a matsayin sabuwar ministar kudi

Shamsuna Ahmad ta kama aiki gdan gadan a matsayin sabuwar ministar kudi

- Zainab Shamsuna Ahmad ta kama aiki gadan gadan a matsayin ministar kudi

- Zainab ta samu wannan mukami ne bayan tsohuwar ministar ta yi murabus

A ranar Litinin, 17 ga watan Satumba ne sabuwar Ministan kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta fara aiki gadan gadan a biyo bayan yin murabus da tsohuwar ministan kudi Kemi Adeousn ta yi daga mukamin a satin daya gabata, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Zainab ta shiga ofis ne bayan kimanin awanni 72 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da ita a matsayin sabuwar ministan kudi bayan Kemi Adeosun ta ajiye aiki a ranar 14 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Sheikh Nakaka ya zama sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai ta Kaduna

Shamsuna Ahmad ta kama aiki gdan gadan a matsayin sabuwar ministar kudi

Shamsuna Ahmad
Source: Depositphotos

Ita dai Shamsuna Ahmad ta kasance karamar ministan kasafi da tsare tsare ne kafin wannan sabon mukamin data samu, haka zalika kafin wannan mukamin, itace shugaban hukumar hake haken ma’adanan kasa.

A yau din da Zainab ta fara aiki an ruwaito ta kwashe tsawon lokaci tana fahimtar yadda zata fara fuskantar gagarumin aikin dake wannan ma’aikata, hakanan an hangeta tana karanta takardun mika mulki da tsohuwar ministan ta bar mata.

Ita dai tsohuwar ministan kudi, Adeosun ta ajiye mukaminta ne biyo bayan wata badakala da ake zarginta da aikatawa na yin takardar shaidar tsallake bautan kasa ta bogi, sai dai tace ba da saninta aka yi hakan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel