Zaben 2019: Kada ku dawo da barayi kan mulki – APC ga yan Najeriya

Zaben 2019: Kada ku dawo da barayi kan mulki – APC ga yan Najeriya

- Jam’iyyar APC ta gargadi yan Najeriya da su zuba idanu sosai a harkokin siyasar kasar

- Tace kada su yi kuskuren dawo da jam’iyyar PDP kan mulki a 2019

- APC tace duk masu neman takara a karkashin jam’iyyar adawar barayi ne

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta hannun babban sakataren labaranta, Nabena Yekini, ta roki mambobin jama’a da su zuba idanu sosai akan harkokin siyasar kasar, inda suka kara da cewa babban jam’iyyar kasar sun dauki hanyar kwace mulki ta hanyar damfara.

A wata sanarwa da Legit.ng ta samu, APC ta gargadi yan Najeriya akan yan siyasa dake amfani da kudaden sata wajen yakin neman zabe don ganin ta cizge gwamnatin Shugaba Buhari mai yakar cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa yan siyasan dake neman takarar kujeru daban-daban a karkashin babban jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), barayi ne, suna son sake dawowa da halinsu na sata ne.

Zaben 2019: Kada ku dawo da barayi kan mulki – APC ga yan Najeriya

Zaben 2019: Kada ku dawo da barayi kan mulki – APC ga yan Najeriya
Source: UGC

Nabena ya bukaci ýan Najeriya da kada su lashe amansu tunda sun yanke shawarar yin yaki da rashawa tare da gwamnatin tarayya.

Ya tunatar da yan Najeriya irin tarin barnar da jam’iyyar PDP tayi a shekaru 16 da tayi tana mulki a kasar.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutane 300 a garuruwan Plateau

Duk da cewar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takara guda a jam’iyyar, Cif John Francis Igwe, shahararren dan kasuwa daga jihar Enugu ya yanki fam din takara domin kalubalantar shugaban kasar wajen samun tikitin jam’iyyar.

Babban dan kasuwan ya bayyana kudirinsa a Abuja ta hannun kakakin kungiyar magoya bayansa, Mista Mbama Mac Anthony, jaridar The Sun ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel