Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Wani matashi ya yi mai amfani da shafin sada zumunta na instagram, @captainblazee ya nuna wani bidiyo aka ce wani dan siyasa a Legas ya sace azzakarin wani mai gadi bayan ya bashi kudi a City Hall.

A cewar @captainblazee, mai gadin ya nemi azzakarinsa ya rasa bayan ya karbi kudi daga hannun dan siyasan kamar yadda muka samu daga shafin Linda Ikeji.

Da ya ke wallafa bidiyon a shafinsa na instagram, ya yi takaicin yadda lamura ke tabarbarewa a Najeriya.

"Ina zamu je a Najeriya! Yayin wata taron siyasa da akayi a City Hall da ke Legas. Wani mai gadi ya yi ikirarin cewa azzakarinsa ya bace bayan wani mutum da ya zo a wata babban motan alfarma ya bashi kudi. Ya yi ta ihu yana neman taimako amma babu wanda ya iya tsayar da motar har da 'yan sanda," inji @captainblazee

Ga bidiyon a kasa.

DUBA WANNAN: An bawa hammata iska yayin rikicin shugabancin APC a Bauchi

Saura kadan mai gadin ya rasa rayuwansa a lokacin da wanda ake zargin ya ke kokarin guduwa a motarsa bayan 'yan sanda sun fara harbin motan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel