Babu wanda ya isa ya tsige ni – Saraki

Babu wanda ya isa ya tsige ni – Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi kurin cewa ba za’a taba tsigeshi ba saboda jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da ke kokarin hakan sune maras rinjaye a majalisar dattawa. Saboda haka ba zai yiwu ba.

Kana kuma ya bayyana cewa ba zai taba murabus daga kujerarsa ba kamar yadda jam’iyyar APC dake bukata.

Saraki wanda yayi hira da manema labarai a garin Minna, jihar Neja yayin cigaba da yawon yain neman zabensa jiya Lahadi, yace:

“Mambobin jam’iyyar APC suna sane cewa mu ke da rinjaye kuma duk abinda suke nufin yi, sun san basu da rinjaye. Wani kaidi da suke yi shine cewa in sauka daga kujeran amma ina tabbatar muku da cewa hakan ba zai yiwu ba kuma ba zai sauka ba.”

Ya caccaki dukkan masu kira ga majalisar dattawa ta yanke hutunta ta dawo, kari da cewa dukkan mambobin majalisar ne suka amince da cewa a tafi hutu bisa ga doka. Saboda haka, majalisar dokokin tarayya bata sabawa doka ba na rashin dawowa ba.

KU KARANTA: Daga karshe, Ganduje ya nada Gawuna matsayin mataimakin gwamna

A bangare guda, tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Ibrahim Babangida, ya tabbatar wa Saraki cewa zai mara masa baya kan kujerar shugaban kasa da yake nema inda yace: “Yanzu lokaci ne inyi maka abinda mahaifinka yayi min.”

“Na tuna lokacin da nike mulki, nayi magana da mahaifinka, Oloye Saraki, wanda ke bani shawara kan abubuwa da ya shafi kasan nan.”

Ana sa ran majalisar dattawa zata dawo bakin aiki ranan 25 ga watan Satumba, 2018.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel