Jam'iyyar People Trust ta fadawa Ambode ya zo su ba sa tikitin zaben 2019

Jam'iyyar People Trust ta fadawa Ambode ya zo su ba sa tikitin zaben 2019

Jam'iyyar People Trust PT wanda babbar Jam'iyya ce da aka kafa bayan an samu hadaka da sauran kananan Jam'iyyu sun nuna goyon bayan su ga Gwamnan Legas Akinwumi Ambode a zabe mai zuwa.

Jam'iyyar People Trust ta fadawa Ambode ya zo su ba sa tikitin zaben 2019

Wata Jam'iyya za ta ba Ambode tikitin takarar Gwamna a 2019
Source: UGC

Babban Lauyan da ke kare hakkin Bil Adama Olisa Agbakoba da kuma Yaron tsohon Shugaban kasa Tafawa Balewa watau Dr. Abduljalil Tafawa Balewa su na tare da Akinwumi Ambode inda har su kayi masa tayin Jam'iyyar su ta PF.

Hakan na zuwa ne bayan an fara kokarin hana 'Dan takarar kuma Gwamna mai-ci tikiti a karkashin Jam'iyyar sa ta APC mai mulki bayan ya samu matsala da tsohon Gwamnan Jihar kuma Mai gidan sa watau Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

KU KARANTA: Buhari ya shiga cikin rikicin Ambode da Tinubu

Kwanan nan ne dai Jam'iyya PT ta shigo gari inda kuma ake yi mata kallon Jam'iyyar 'yan bana-bakwai a siyasar Najeriya. Jam'iyyar mai jama'a da-dama ta nuna cewa a shirye ta ke ta marawa Akinwumi Ambode baya a 2019.

Wani babba a Jam'iyyar ya yabawa irin kokarin da Ambode yayi a kan kujerar Gwamna don haka yace akwai bukatar ya zarce domin ya cigaba da aikin da yake yi. Jam'iyyar tace Ambode matashi ne wanda ya san aiki irin wanda ake nema.

Jiya kun ji cewa Gwamna Akinwumi Ambode ya ruga zuwa babban Birnin Tarayya Abuja domin ya gana da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a game da zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel